Inter Milan tana sa ran Chelsea ta biya ta £110m kan dan wasan Belgium mai shekara 28 Romelu Lukaku bayan da ta yi watsi da tayin farko na £85m da karin dan wasan Sifaniya Marcos Alonso, mai shekara 30. (Mail)
Yiwuwar tafiyar Jack Grealish Manchester City za ta iya sa wa Bernardo Silva ya bar kungiyar, inda ake sa ran Barcelona da Atletico Madrid za su yi wawason dan wasan tsakiyar na Portugal mai shekara 26. (Mundo Deportivo – in Spanish)
Ana sa ran Aston Villa ta nemi daukar dan wasan Norwich da Ingila Todd Cantwell, mai shekara 23, idan Grealish ya kammala tafiya Etihad Stadium a kan £100m. (Sky Sports)
Atalanta za ta tattauna da Chelsea a karshen makon nan domin duba yiwuwar kulla yarjejeniya kan dan wasan Ingila Tammy Abraham, mai shekara 23. (Gianluca di Marzo)
Paul Pogba zai soma kakar wasan bana a Manchester United amma zai yanke shawara game da makomarsa kafin a rufe kasuwar musayar ‘yan kwallo, a yayin da har yanzu PSG take son daukar dan wasan na Faransa mai shekara 28.
Tottenham tana son sayen dan wasan da ke kai hari daga tsakiya a bazarar nan inda take sa ran daukar dan wasan PSV Eindhoven da ke buga wa Ingila gasar ‘yan kasa da shekara 21 Noni Madueke, mai shekara 21, da dan wasan Sampdoria dan kasar Denmark Mikkel Damsgaard, mai shekara 21. (Standard)
Dan wasan Barcelona dan kasar Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 28, yana cikin ‘yan wasan da Tottenham take son dauka idan ta sayar da Harry Kane, mai shekara 28. (Mundo Deportivo – in Spanish)
Ana sa ran Lionel Messi zai sanya hannu a kan sabuwar kwangilarsa a Barcelona a cikin wannan makon. Kwangilar dan wasan mai shekara 34 ta kare a watan jiya amma dan kasar ta Argentina ya fada da bakinsa cewa ya amince zai tsawaita zamansa a kungiyar da karin shekara biyar kuma za a rage kashi 50 na alawus dinsa. (Sky Sports)
Leicester City ta ki amincewa da tayin Arsenal na ba ta wasu ‘yan wasa tare da kudi domin karbar dan wasan tsakiyar Ingila James Maddison, mai shekara 24. Rahotanni sun ce Leicester ba ta son ‘yan wasan da Gunners suke son ba ta domin yin musayar. (Football Insider)
Yunkurin Chelsea na daukar dan wasan Sevilla Jules Kounde ya ci tura saboda dan wasan Faransa Kurt Zouma, mai shekara 26, wanda take fatan sayarwa domin samun gurbin dan wasan mai shekara 22, ya ki amsa tayin tafiya West Ham. (Guardian)
Newcastle ta nuna sha’awar karbar aron dan wasan Ingila da ke buga gasar ‘yan kasa da shekara 21 Oliver Skipp, mai shekara 20, daga Tottenham. (Mail)
Post comments (0)