Shahararriyar tsohuwar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Rahama Hassan ta dawo cikin abokan sana’arta bayan dogon lokaci.
Tun kafin jarumar ta yi aure ba’a kara jin doriyarta ba a masana’antar ta shirya fim harma ga shafukan soshiyal midiya.
Kwatsam yanzu sai ga wasu bidiyonta sun bayyana a shafukan sadarwar zamani sanye da hular 13X13 kuma cikin mambobin kungiyar nan ta 13X13.
13×13 kungiya ce da ta hada fitattun manyan fasihan mawakan Kannywood, wadanda su ne kashin bayan tafiyar, sannan akwai fitattun daraktoci, furodusoshi da kuma ‘yan wasa da sauran su a cikinta.
Harma akwai wani bidiyo da babban furodusa Mallam Abubakar Bashir Maishadda ya wallafa a shafinsa na tiktok dauke da rubutun ‘Rahama Hassan is back’ wato Rahama Hassan ta dawo.
Rahama bata dawo fim ba, mamba ce a kungiyar 13X13 – Maishadda
Sai dai yan Jarida sun tuntube shi don jin ko da gaske Rahama Hassan ta dawo harkar fim, Maishadda ya tabbatar da kasancewar jarumar a cikin kungiyar ta 13X13 amma ya ce bata dawo harkar fim ba.
Maishadda ya ce:
“Bata dawo fim ba amma mamba ce a kungiyar 13X13.”
Post comments (0)