- Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar wani bidiyo na jarumar Kannywood, Umma Shehu tare da diyarta suna rawa da waka
- Da dama sun yi tir da bidiyon yayin da suke ganin hakan bai dace ba ga uwa wacce ita ce mai bayar da tarbiya ga yaranta
- Hakan na zuwa ne yan kwanaki bayan jarumar ta fito ta yi martani ga masu zaginta, inda ta ce suna ji suna gani za ta shige aljannah ta barsu a madakata
Wani bidiyo na shahararriyar jarumar Kannywood, Umma Shehu, ta haifar da cece-kuce a shafukan soshiyal midiya.
A cikin bidiyon wanda mufeeda_rasheed ta daura a shafinta na Instagram, an gano jarumar tare da diyarta suna rawa tare da rera wata wakar soyayya.
Sai dai hakan bai birge wasu ba inda suka ta yin suka kan cewa wanene zai yiwa wani fada a tsakanin uwar da yar tata.
Kamar yadda kuka sani ba wannan bane karo na farko da jama’a ke yin caaa a kan jarumar, domin tana daya daga cikin jarumai mata da ake bibiyar duk wani motsinsu domin ganin sun yi dan kuskure.
Sai dai ga dukkan alamu hakan bai taba damun jarumar ba domin duk da sukan da take yawan ya, baya hana mata yin abubuwan da ta sa gaba da sunan gudun maganar mutane.
Post comments (0)