
Zanga-zanga ta ɓarke a Iraki bayan gobarar da ta hallaka mutum 60 a asibiti
ye da mutum 60 ne suka mutu bayan da gobara ta tashi a sashen da aka keɓe don jinyar masu cutar korona a wani asibiti a birnin Nasiriya na ƙasar […]
Tarihin Garin Kadawa
Bello Sani
Sarkin Noman Daura Bello Sani
Masarautar Daura Bello Sani
Sauraremu Kai Tsaye Bello Sani
Wata sabuwar dambarwar siyasa ta kunno kai a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, bayan wata gayyata da majalisar dokokin jihar ta yi wa mataimakin gwamnan jihar, domin ya bayyana a gabanta don yin bayani a kan gaba gaɗin da ya yi wajen shirya wani taro da take zargin na siyasa ne duk da jami’an tsaro sun hana shi yi.
Majalisar dai tana zargin Barista Mahdi Aliyu da nuna halin ko in kula ga yanayin da jihar ke ciki na matsalar tsaro, da kuma yin abin da ka iya haddasa tarzoma a jihar.
Yayin wata hira da BBC Hausa, kakakin majalisar Nasiru Mu’azu Magarya, ya ce wani dan majalisa Yusuf Alhassan Kanoma ne ya gabatar da kuduri don ganin an gayyaci mataimakin gwamnan ya je ya yi bayani kan wannan zargi da ake yi masa.
Kakakin majalisar ya ce ”Kuskure ne a halin da ake ciki ace a zo a gabatar da taro don yana da hadari ga tsaro, kuma ‘yan ta’adda na iya amfani da wannan dama domin su cutar da al’umma”
To sai dai duk da wannan wannan gayyata, mataimakin gwamnan jihar ta Zamfara ya ce zuwa yanzu a kafofin yada labarai kawai yake jin cewa an gayyace shi, amma babu wanda ya sanar da shi hakan a hukumance.
Me PDP ta ce kan batun ?
ASALIN HOTON,DEPUTYGOVZAMFARASTATE
Tuni jam’iyyar hamayya ta PDP a jihar ta yi martani kan batun, inda shugaban riko na jam’iyyar a jihar ya ce taron da ake zargin mataimakin gwamnan ya yi bashi da alaka siyasa, domin babu wata shaida da ke nuna cewa na siyasa ne.
”Idan aka ce taron siyasa ai za a ga an gabatar da taro, za a ga takardun gayyatar mutane zuwa taron, amma babu ko daya da aka gani, taro ne da masoyansa suka tare shi don yi masa barka da zuwa, kuma laifi ne idan masoyinka ya zo ya ce maka barka da zuwa ?” inji shi.
Ya ce a halin da ake ciki suna jira ne suga takardar gayyatar kafin sanin matakin da za su dauka, ”mu yanzu baza mu yi riga malam masallaci ba, har sai mun ga takarda” a cewarsa.
A ƙarshen watan Yunin da ya gabata ne dai gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya jagoranci yawancin ‘yan majalisar dokokin jihar da ma na tarayya wajen sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, kuma a lokacin an gudanar da gagarumin taron siyasa da ya tara gwamnonin jam’iyyar APC da dama, lamarin da ya sa aka fara tunanin ko ba daɗe ko ba jima sai ya raba gari da mataimakinsa, wanda ya zabi ci gaba da zama a jam’iyyar PDP.
ye da mutum 60 ne suka mutu bayan da gobara ta tashi a sashen da aka keɓe don jinyar masu cutar korona a wani asibiti a birnin Nasiriya na ƙasar […]
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)