
‘Allah baya tare da kai’: Wani mutum ya faɗa wa Fafaroma a cikin taron mutane
A wani yanayi mai ban mamaki, wani mutum, a Birnin Vatican ya bude baki ya fada wa Fafaroma Francis cewa ‘Allah baya tare da shi’ Lamarin ya faru ne a […]
Tarihin Garin Kadawa
Bello Sani
Sarkin Noman Daura Bello Sani
Masarautar Daura Bello Sani
Sauraremu Kai Tsaye Bello Sani
Bashir Sani February 2, 2022 34
Jihar Kano – Hukumar Kula da Jami’o’i ta Najeriya, NUC, ta amince a fara gudanar da karatun digiri a bangaren shari’ar musulunci a Jami’ar Bayero da ke Kano, BUK, rahoton The Cable.
Hukumar ta kuma amince da wasu kwasa-kwasai 11 a tsangayar ilimi wato education.
Shari’a na daga cikin ginshikin addinin musulunci.
Hukunce-hukuncen shari’a sun samo asali ne musamman daga Al-Kurani mai girma, hadisan manzon Allah (SAW).
JAMB ta sanar da amincewar cikin sanarwar da ta fitar a ranar 31 ga watan Janairu a shafinta na intanet.
A cewar sanarwar, an amince Jami’ar BUK ta fara Digiri na Shari’a wato B.A. Shari’a.READ ALSOJerin fitattun ciniki 12 da aka yi zuwa ranar karshen cefanen ‘Yan wasa a Turai a 2021/22
Ita kuma Kwallejin Ilimi ta Tarayya da ke Kano, an amince mata fara wasu kwasa-kwasai na hadin gwiwa guda uku.
Su ne B.A. (Ed.) Islamic Studies; B.Sc. (Ed.) Biology Education da B.Sc (Ed.) Chemistry Education.
Ita kuma Kwallejin Ilmi ta Minna, kwasa-kwasan hadin gwiwa da aka amince mata fara sun kunshi B.A. (Ed.) History Education, B.A. (Ed.) Hausa Education da B.A. (Ed.) Arabic Education, B.A. (Ed.) Islamic Studies.
Saura sun hada da B.Sc. (Ed.) Biology Education, B.Sc.(Ed.) Mathematics Education and B.Ed. Social Studies da B.A. (Ed.) English Education.
A baya-bayan nan hukumar ta amince da kafa wasu karin jami’o’i biyu a Jihar Legas.
Saurari karin bayani …
A wani yanayi mai ban mamaki, wani mutum, a Birnin Vatican ya bude baki ya fada wa Fafaroma Francis cewa ‘Allah baya tare da shi’ Lamarin ya faru ne a […]
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)