play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Hukumar ‘Yan sanda ta tabbatar da kisan Mutane 90 a sabon harin da aka kai jihar Zamfara

Labarai

Hukumar ‘Yan sanda ta tabbatar da kisan Mutane 90 a sabon harin da aka kai jihar Zamfara

Bello Sani June 12, 2021 4


Background
share close

Hukumar Yan sanda a jihar Zamfara ta tabbatar da harin da aka kai a karamar Hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara, inda akayi asarar rayukan mutum Casa’in

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) a jihar, SP Shehu Mohammed, ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Gusau ranar Juma’a.

“Tabbas, zan iya tabbatar muku da cewa an kai wani hari a kauyen Kadawa da ke karamar hukumar Zurmi inda ‘yan ta’adda suka bi dare wajen kai hari kan mutanen da ba’a sani ba suka kashe su cikin ruwan sanyi, ” Inji Mohammed.

“Da samun labarin harin, Kwamishinan‘ yan sanda, CP Hussain Rabiu, ya umarci hadin gwiwar jami’an tsaro da su dunguma zuwa yankin, domin su dawo da zaman lafiya da kwarin gwiwa a tsakanin al’ummomin tare da bin diddigin wadanda suka aikata laifin domin hukunta su.

“Kwamishinan, tare da shugaban majalisar dokokin jihar, Alhaji Nasiru Magarya, sun je wurin da abin ya shafa don yi wa iyalai ta’aziyya,” in ji shi.

NAN ta tattaro Bayanai daga wasu shaidun gani da ido da ke kauyen cewa ‘yan fashin sun mamaye kauyen da tsakar ranar Alhamis, suna magana cikin harshen da bama fahimta tare da harbin duk wani wanda ke kokarin tserewa annobar.

Daya daga cikinsu wanda ya bayyana sunansa Lawali ya ce an gano gawarwaki 67 a cikin kauyen yayin da aka tsince wasu 26 a wurare daban-daban da ke gefen kauyen tare da jikkata wasu da dama.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *