play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Gwamnatin Tarayya ta bayyana dalilai 3 da suka sa aka dakatar da kafar sadarwar Twitter

Labarai

Gwamnatin Tarayya ta bayyana dalilai 3 da suka sa aka dakatar da kafar sadarwar Twitter

Bello Sani June 5, 2021 12


Background
share close

Biyo bayan dakatarwar da aka yi wa kamfanin Twitter a Najeriya, gwamnatin tarayya ta bayyana dalilan da suka sa aka dakatar da ayyukan shafin.

1. An dakatar da amfani da shafin Twitter saboda maslahar Najeriya

2. Gwamnati ta zargi shafin sada zumuntar da yin kafar ungulu ga ka’idar kasancewar kamfanonin Najeriya

3. Ministan ya kuma bayyana cewa dakatarwar na daga cikin dokokin gudanarwar hukumar kula da gidajen rediyo da talbijin ta ƙasar NBC na dukka OTT da kafofin sada zumunta a Najeriya.

Dakatar da ayyukan Twitter a Najeriya na zuwa ne jim kadan bayan da gwamnatin tarayya ta soki katafaren kamfanin na sada zumunta kan share wani rubutu da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wanda ya yi gargadi kan tsauraran matakai a kan masu ballewa.

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, a ranar Laraba, 2 ga Yuni, ya zargi shafin na dada zumunta da nuna son kai a kan batutuwan da suka shafi lamuran cikin gida na Najeriya.

Ya ce akwai ayar tambaya a rawar da Twitter ke takawa kuma Najeriya ba za ta yarda a yaudare ta ba.

A wani labarin, kamfanonin sadarwa a Najeriya kamar MTN, Glo, Airtel da 9mobile sun fara rufe amfani da damar shiga dandalin sada zumunta twitter, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kamfanonin sun ce sun samu saƙon umarni daga hukumar sadarwa ta ƙasa NCC cewa su tsayar da damar shiga twitter a ƙasa biyo bayan umarnin gwamnatin tarayya na dakatar da shafin.

Yan Najeriya masu amfani da twitter sun wayi garin ranar Asabar ba tare da samun damar amfani da shafinsu na twitter ba, yayin da wasu ke amfani da wata manhajar sadarwa domin shiga shafin su.

 

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *