
Zaben 2023: ‘Tsarin karɓa-karɓa ba zai yi tasiri tsakanin APC da PDP ba’
Wani jigo a jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ya bayyana cewa babu wata jam’iyya da tsarin karɓa-karɓa zai fidda ita a zaɓen shekara ta 2023 – batun da ke […]
Tarihin Garin Kadawa
Bello Sani
Sarkin Noman Daura Bello Sani
Masarautar Daura Bello Sani
Sauraremu Kai Tsaye Bello Sani
Gwamnatin Najeriya ta ce ma’aikatar lafiya na yunƙurin fara amfani da allurar Depot Medroxyprogesterone Acetate Subcutaneous domin ƙarfafa tsarin iyali a ƙasar, a cewar rahoton kamfanin labarai na NAN.
Ƙaramin Ministan Lafiya Olorunimbe Mamora ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da shirin gwamnatin tarayya na tsarin iyali ga kafafen yaɗa labarai, wanda aka yi ta intanet ranar Alhamis.
“Wannan wata hanya ce ta haɓaka samar da kayayyakin tsarin iyali domin bai wa ‘yan Najeriya damar yin zaɓi da kansu,” in ji shi.
“Maganin wanda ake bai wa mutane damar yi wa kansu allura da kansu, ana kallonsa a matsayin wanda zai kawo gagarumin sauyi a harkokin tsarin iyali a Najeriya.
“Yana amfani matuƙa wajen tabbatar da ɗorewar amfani da magani musamman a ƙauyuka ta hanyar bai wa mutum kwalaben maganin bayan an ba shi horo kan yadda za a yi amfani da shi.”
Wani jigo a jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ya bayyana cewa babu wata jam’iyya da tsarin karɓa-karɓa zai fidda ita a zaɓen shekara ta 2023 – batun da ke […]
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)