Kano – Babbar Kotun jihar Kano ta fara shirin yanke hukunci game da shari’ar kisan Hanifa Abubakar yar kimanin shekara biyar a duniya, kamar yadda Aminiya ta ruwaito.
Kotun ta yi watsi da ikirarin wanda ake zargi na farko, Abdulmalik Tanko, wanda ya canza maganarsa ta farko, inda ya ce ba shi ne ya kashe Hanifa ba.
Rahoto ya nuna cewa yanzu haka, Kotun ƙarkashin jagorancin mai shari’a Usman Na’abba, na shirin yanke hukunci kan kisan daliba Hanifa.
Alƙalin Kotun na shirin yanke hukunci ne bayan gamsuwa da cewa babu wanda ya tilasta wa wanda ake zargi, shugaban makaranta, Abdulmalik Tanko, ya amince shi ya kashe yarinyar.
Tun da farko Tanko ya roki Kotun ta yi watsi da kalamansa na farko da ya amsa kisan Hanifa, ya kuma kafa hujja da cewa ya yi haka ne domin ceton rayuwarsa daga azabtarwan yan sanda.
Yayin zaman cigaba da sauraron ƙarar, Tanko ya shaida wa Kotu yadda yan sanda suka rinka azabtar da shi kuma suka masa barazanar kisa matukar bai amsa laifin da ake tuhumarsa ba.
Sai dai bayanan Tanko ya saɓa wa matar da ake zargin su tare, Fatima Jibrin, wacce ta bayyana cewa masu binciken sun ba ta tsoro amma ba su duke ta ba.
A nasu bangare, yan sandan da suka gudanar da bincike sun musanta zargin Tanko, tare da faɗa wa Kotu cewa sun bi hanyoyin da ya dace wajen karban bayanan mutanen da ake zargin.
Post comments (0)