play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Addini
  • keyboard_arrow_right Da Dumi-Dumi: An Sanar Cewa Ba A Ga Watan Karamar Sallah Ba a Najeriya

Labarai

Da Dumi-Dumi: An Sanar Cewa Ba A Ga Watan Karamar Sallah Ba a Najeriya

Bello Sani May 11, 2021 25


Background
share close

Sanarwar kwamitin ganin wata a Najeriya ta bayyana cewa, ba a alamar watan Shawwal ba. An sanar cewa, gobe za a tashi da azumi na 30 domin cike watan Ramadanan bana da zai kai kwanaki 30. Daga sanarwar, a fahimci cewa, Alhamis, 13 ga watan Mayu za ta kasance ranar karamar sallah

Kwamitin Sarkin Musulmi kan harkokin addini tare da hadin gwiwar Kwamitin Duban Wata a Najeriya sun sanar da cewa ba su samu labarin ganin watan Shawwal a Najeriya ba a yau Talata 11 ga watan Mayun wanda ya yi dai-dai da 29 ga watan Ramadana.

Don haka Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar CFR, ya ayyana Alhamis 13 ga watan Mayu 2021 a matsayin ranar Sallah kuma 1 ga watan Shawwal.

Sarkin Musulmi ya taya Musulmin Najeriya murna tare da fatan Allah ya yi masu albarka.

Sanar da Legit.ng Hausa ta gano a shafin kwamitin na Tuwita ya karanta: “Babu alamar ganin watan Shawwal a Najeriya yau Talata 11 ga Mayu, gobe Laraba 12 ga Mayu shi ne 30 ga Ramadan. Nan gaba kadan za a fitar da wata sanarwa a hukumance daga majalisar.

A wani labarin, A yau 11 ga watan Mayu ne aka cika kwanaki 29 ana azumtar watan Ramadana mai alfarma, kuma ake sa ran ganin watan Shawwal domin ajiye azumin tare da fara bikin karamar Sallah.

Mun kawo muku jerin kasashen da suka sanar da yin azumi 30, wato sallah karama a wadannan kasashen sai ranar Alhamis 13 ga watan Mayu 2021, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

 

Tagged as: , .

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *