play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Tsaro
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Bello Muhammad Matawalle: Mun kama masu kwarmata wa ƴan bindiga bayanai fiye da 100 a Zamfara

Tsaro

Bello Muhammad Matawalle: Mun kama masu kwarmata wa ƴan bindiga bayanai fiye da 100 a Zamfara

Bello Sani September 14, 2021 6


Background
share close

Gwamnatin Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta kama masu kwarmata wa ƴan bindiga bayanai ‘informants’ fiye da 100 tun bayan katse layukan sadarwa a faɗin jihar.

Gwamnan Jihar Dr Bello Muhammad Matawalle ne ya bayyana haka cikin wata hira ta musamman da BBC a gidansa da ke Gusau babban birnin jihar.

“Toshe duk wata hanyar sadarwa tsakanin masu kwarmata bayanai ga ƴan bindiga ya yi tasiri sosai domin yanzu mun kama infoma fiye da 100,” in ji gwamna Matawalle.

Tsawon kwana 11 kenan da aka toshe layukan salula a fadin Zamfara, daga cikin matakan da hukumomi suka ɗauka na ƙoƙarin magance matsalolin taro a jihar.

Matakin toshe layukan na sadarwa ya shafi yankunan jihar Katsina da ke makwabtaka da jihar Zamfara.

Gwamna Matawalle ya yi ikirarin cewa tun toshe hanyoyin sadarwa da aka yi a faɗin Zamfara “babu wani babban abin da ya faru,” yana mai cewa “ƴan bindiga sun koma suna yi wa wadanda suka sace bulala a madadin kuɗin fansa da suka rasa.”

Yadda aka ceto ɗaliban Kayar Maradun

Gwamna Matawalle ya yi bayanin yadda aka kuɓutar dalibai fiye da 70 da ƴan bindiga suka sace daga wata makaranta a garin Kayar Maradun garinsa na haihuwa makwanni biyu da suka gabata.

Gwamnan ya ce an ceto ɗaliban ne ta hanyar amfani da tubabbu waɗanda gwamnati ta yi sulhu da su. “Kuma a lokacin Allah ya ba ni fasahar tunanin rufe network, saboda ga dukkan bincike na babu babbar illa kamar sadarwa ga yan ta’adda.”

“Bayan tsinke layuka, ɗayadaga cikin waɗanda muka yi sulhu da su ya yi alkawalin cewa zai gano inda ɗaliban suke kuma muka yarda aka ceto su.”

“Yana gano su. nan take muka ɗauki mataki cikin dare muka tura jami’an tsaro aka kwato su,” in ji Matawalle.

Gwamnan kuma ya ce ba wani maganar sasanci da aka yi da ƴan bindigar, da aka tambaye shi ko an yi amfani da ƙarfi ne wajen ceto ɗaliban.

‘An yaudare mu’

Tun hawansa mulki gwamna Matawalle yake ɗa’awar sulhu da ƴan bindiga da suka addabi jiharsa.

A hirarsa da BBC, Matawalle ya ce bai kamata yana hawa gwamna ya shiga yaƙi da yan bindiga ba, don haka ya yi sulhu ne domin ba su haƙƙinsu.

Sai dai gwamnan ya ce daga baya ya gano akwai yaudara.

“Daga baya yaudara ta shiga domin sun tafi suna kai wa mutane hari – na ga cewa yanzu bari mu yanke hanyar da suke samun abinci da sadarwa.” in ji shi.

Cikin wani bidiyo da ke ta yawo a kafafen sada zumunta, an ga Gwamna Matawalle yana jawabi a wani masallaci bayan idar da sallah, inda yake cewa ‘yan bindiga sun yi watsi da damar da suka samu ta sulhu a baya, yanzu tsakanin gwamnati da su sai aikawa lahira.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *