play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Addini
  • keyboard_arrow_right Babban Limamin Ibadan Ya Bijire Wa Sarkin Musulmi, Ya Yi Sallar Idi

Labarai

Babban Limamin Ibadan Ya Bijire Wa Sarkin Musulmi, Ya Yi Sallar Idi

Bello Sani May 12, 2021 10


Background
share close

Sheikh AbdulGaniy Agbotomokekere, babban limamin Ibadanland, ya jagoranci wasu Musulmai yin sallar Idi a Ibadan

Sultan na Sokoto, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya sanar a ranar Talata, 11 ga watan Mayu, cewa ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a Najeriya

Abubakar ya bukaci Musulmi da su tashi da azumin Ramadana a ranar Laraba, 12 ga watan Mayu

Babban Limamin Ibadanland, Sheikh AbdulGaniy Abubakar Agbotomokekere, a ranar Laraba, 12 ga Mayu, ya bijire wa umarnin da Sarkin Musulmi ya bayar na yin azumi saboda rashin bayyanar sabon jinjirin watan Shawwal.

Sheikh Agbotomokekere ya jagoranci wasu yan tsirarun musulmai don yin sallah a yankin Agodi da ke tsohon garin.

Mai kula da harkokin yada labarai na Limamin, Ustadh Idris Agbotomokekere, ya ce umarnin Babban Limamin na kan ganin sabon jinjirin wata.

Amma, malamin ya yi abin da ya saba wa maganar Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya karkashin jagorancin shugabanta-Janar kuma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar.

Sultan din a ranar Talata 11 ga Mayu, ya sanar da Musulman Najeriya cewa saboda rashin bayyanar jinjirin wata da ke nuna farkon watan Shawal, Ramadan zai kare a ranar Laraba, 12 ga Mayu.

Don haka, aka shirya gudanar da sallar Idi a ranar Alhamis 13 ga watan Mayu, a cewar wani bayani daga Sarkin Musulmi.

Umarnin na Sultan ya yi daidai da fikihun Musulunci na kidayar Ramadan zuwa 30 idan ba a ga Shawwal ba.

Sai dai, Sheikh Agbotomokekere ya jagoranci wasu musulmai muminai don yin Idi wanda ya kawo karshen azumin Ramadhan.

Daga cikin manyan da suka halarci idin tare da Limamin sun hada da mataimakin gwamnan jihar Oyo, Injiniya Rauf Olaniyan, shugaban jam’iyyar PDP na shiyyar, Cif Taofeek Arapaja da sauransu.

Da yake magana da Legit.ng, mai kula da shafukan sada zumunta na Babban Limamin na Ibadanland, Ustadh Idris Agbotomokekere, ya ce shawarar da Babban Limamin ya yi na bikin Idi ya biyo bayan matsayinsa na shugaban kungiyar limamai da malamai a Ibadanland.

A gefe guda, shahararren malamin nan na addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya gabatar da sallar Idi tare da dimbin mabiyansa ranar Laraba, 12 ga watan Mayu.

An tattaro cewa Shehin Malamin ya gudanar da sallar Idi ne a gidansa da ke garin Bauchi.

Sashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa daya daga cikin ‘ya’yan malamin, Tijjani Sheikh Dahiru Bauchi, shi ne ya ja sallar ta Idi yayin da malamin yake cikin mabiya sallan.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *