play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Tsaro
  • keyboard_arrow_right An Kama Fasto Da Wasu Mutum Biyu Da Naira Miliyan 15 Na Kuɗaɗen Jabu a Otel

Labarai

An Kama Fasto Da Wasu Mutum Biyu Da Naira Miliyan 15 Na Kuɗaɗen Jabu a Otel

Bello Sani July 8, 2021


Background
share close

Yan sanda sun kama wasu mutum uku da ake zargi da mallakar kudin jabu fiye da Naira miliyan 15 Mutanen dai sune Fasto Sabastine, Emmanuel Aka Zuwa da wani Umar Mohammed da aka kama a Otel Wadanda ake zargin sun amsa laifin mallakar kudin jabun suna mai cewa wani Nifom ne ya sayar musu da kudin jabun a Makurdi Ƴan sanda a jihar Niger sun yi holen wasu mutane uku da ake zargi da mallakar kudaden jabu ƴan dubu-dubu da adadinsu ya kai Naira miliyan 15.8, Guardian NG ta ruwaito. Wadanda ake zargin sune Fasto Sabastine Dabu, ɗan shekara 48 daga Zuru, jihar Kebbi, Emmanuel Aka Zuwa, ɗan shekara 42 daga ƙauyen Adi, ƙaramar hukumar Buruku, jihar Benue da Umar Mohammed, ɗan shekara 50 daga Pandagori, ƙaramar hukumar Rafi, jihar Niger.

Guardian ta ruwaito cewa yayin horen wadanda ake zargin a hedkwatar yan sanda a Minna, kakakin yan sanda Wasiu Abiodun ya yi bayanin cewa ƴan sandan ƙaramar hukumar Kontagora, jihar Niger ne suka kama su. Ya ce: “Emmanuel, wanda shine jagaba wurin kitsa laifin an kama shi da N15.830 million wato Naira miliyan sha biyar da dubu ɗari takwas da talatin, a Otel a Kontagora, tare da Fasto Sabastine da Umar Mohammed da ake zargin wakilin Emmanuel ne.” Kakakin yan sandan ya ce Emmanuel ya amsa cewa ya aikata laifin, yana mai ikirarin cewa ya siya kudin bogin a kan N15,000 daga wani Nifom a Katsina Ala jihar Benue. (Wanda yanzu ake nema).

 

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *