
Buhari ya naɗa sabon babban hafsan sojin ƙasan Najeriya
Buhari ya naɗa Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon babban hafsan sojin ƙasan Najeriya. Rundunar sojin ƙasar ce ta sanar da hakan a shafinta na Tuwita a yau Alhamis. […]
Tarihin Garin Kadawa
Bello Sani
Sarkin Noman Daura Bello Sani
Masarautar Daura Bello Sani
Sauraremu Kai Tsaye Bello Sani
An samu labarin cewa, cikin mutane kusan 200 da suka nutse a hadarin jirgin ruwan Kebbi, an gano gawarwaki 13. Rahoton wata majiya ya bayyana cewa, an ceto wasu mutane 20 yayin da wasu masu aikin ceto suka yi aikin ceto
An ce jirgin ya dauko kayan da ya fi karfinsa ne, wannan yasa aka samu barakar da ya jawo kifewarsa
Rahotanni sun bayyana cewa, an gano karin gawarwaki 13 daga cikin fasinjojin jirgin ruwan da ya kife a Jihar Kebbi.
Tun a ranar Laraba aka gano gawarwaki biyar bayan hatsarin jirgin da ke dauke da kusan mutum 200 daga Jihar Kebbi zuwa Neja.
Jirgin ruwan ya kife ne a yankin Tsohuwan Labata da ke Karamar Hukumar Ngaski ta Jihar Kebbi, bayan sa’o’i da fara tafiyar.
Wani mazaunin kauyen Warra, Adamu Umar Warra, ya shaida wa wakilin Aminiya ta waya cewa ana sa ran masu aikin ceto za su gano karin gawarwaki.
Manajan yankin na National Inland Waterways Authority (NIWA) a Yauri, Yusuf Birma, ya shaida wa manema labarai cewa hatsarin ya afku ne saboda lodin da ya fi karfin jirgin, ya kara da cewa an gano gawarwaki hudu.
Jami’in ya ce an ceto mutane 20 “kuma mutane 156 da suka bata ana fargabar sun mutu”.
Jirgin ruwan kuma na dauke da babura kirar Bajaj 30, in ji Mista Birma, Premium Times ta ruwaito.
A wani labarin, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, Sama’ila Dikko, ya ce dole ne Fulani makiyaya da ke shigowa jihar ta Kano su samu izini daga rundunar ‘yan sanda ta jihar da za su baro zuwa Kano.
Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan taron gaggawa na tsaro tare da shugabannin hukumomin tsaro a ofishinsa a ranar Laraba, Mista Dikko ya ce duk wani Bafulatani makiyayi da ya shigo Kano ba tare da izinin ba za a mai dashi in da ya fito, in ji Daily Nigerian.
Ya ce wannan shawarar na daga cikin tsare-tsaren tsaro da rundunarsa ta yi a kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.
Buhari ya naɗa Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon babban hafsan sojin ƙasan Najeriya. Rundunar sojin ƙasar ce ta sanar da hakan a shafinta na Tuwita a yau Alhamis. […]
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)