
Tarihin Garin Kadawa
Bello Sani
Sarkin Noman Daura Bello Sani
Masarautar Daura Bello Sani
Sauraremu Kai Tsaye Bello Sani
A ranar 7 ga watan Yulin 2020 ne aka samu rahotan cewar kimanin mutum sama da 200 sun kamu da cutar amai da gudawa a ƙauyuka 16 da ke yankin karamar hukumar Rano a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Hukumomi a yankin karamar hukumar Rano sun alaƙanta ɓullar cutar da gurɓataccen ruwan sha da rashin tsaftar muhalli.
Kano dai na daga cikin jihohi a Najeriya da ake fama da cutar ta amai da gudawa a baya-bayan nan.
Cutar kwalera ta amai da gudawa na cikin cutuka da ke yin kisa a duniya.
A kan kamu da kwalara sakamakon shan gurbataccen ruwan sha da abinci ko kuma kazanta.
Cutar kwalara galibi ana samun ta ne a cikin ruwa ko kuma a cikin abinci gurɓatacce. Cutar na iya faruwa kuma ta bazu a wuraren da ke da rashin tsafta da gurɓataccen ruwan sha.
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta CDC ta ce ƙasashe da dama na Afirka ne ke fama da kwalera kuma ta kasance musabbabin haifar da cututtuka da mutuwa a ƙasashen.
Saboda girman cutar ne ya sa hukumomin lafiya na duniya suka samar da riga-kafin kwalera.
A wannan maƙala, BBC ta yi nazari kan cutar don ilimintar da mutane.
Mece ce cutar kwalara
Cutar kwalara cuta ce mai saurin yaɗuwa, da ke haifar da amai da gudawa sakamakon ƙwayoyin cutar hanji.
A cikakken bayanin da CDC ta yi kan kwalara ta ce kusan mutum miliyan uku ke kamuwa da cutar duk shekara kuma tana kashe mutum 95,000 duk shekara a duniya.
Ana iya kamuwa da cutar ba tare da nuna wani alamu ba, amma kuma takan iya yin tsanani.
Alƙalumman CDC sun nuna cewa mutum ɗaya cikin 10 da suka kamu da cutar kwalara za ta iya yin tsanani da nuna alamu na amai da gudawa sosai da kuma mutuwar jiki.
Waɗanda cutar ta yi wa tsanani za su yi fama da rashin ruwan jiki wanda zai kai ga haddasa babbar matsala kuma idan ba a yi gaggawar magani ba mutum na iya mutuwa.
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce wajajen ƙarni na 19 kwalara ta bazu a sassan duniya daga Indiya. Miliyoyin mutane ne suka mutu a sassan duniya sakamakon ɓarkewar annobar sau shida.
WHO ta ce ɓarkewar annobar karo na bakwai ta faro ne daga Kudancin Asia a 1961, ta bazu zuwa Afirka a 1971 da kuma a yankin Amurka 1991.
Yanzu kwalara kuma ta bazu a sassan duniya.
Mutum na iya kamuwa da cutar kwalara ta hanyar shan gurɓataccen ruwa ko abinci. Kuma a lokacin annobar, wanda ya harbu na iya ƙara gurɓata ruwa da abinci.
Cutar kuma na iya bazuwa cikin sauri a yankunan da ba a ɗauki matakan tsabtace ruwan sha ba da agudanan ruwa.
Sai dai kuma Hukumar CDC ta ce yana da wahala cutar ta yaɗu daga wani mutum zuwa wani, don haka mu’amula da wanda ya kamu da kwalara ba ya cikin hatsarin kamuwa da cutar.
Mutanen da ke rayuwa a wuraren da babu ruwa mai tsabta da rashin tsaftar muhallai sun f hatsarin kamuwa da kwalara.
Alamomin kwalara sun haɗa da yawan amai da gudawa (ba-haya mai ruwa sosai) da rashin karfin jiki da ƙishi ruwa.
Alamomin kuma sukan ɗauki kwana biyu zuwa uku kafin su bayyana bayan mutum ya harbu da cutar. Wani lokaci yakan kai kwana biyar kafin bayyanar cutar.
Likitoci sukan gudanar da bincike ta hantar ɗaukar samfurin ba-haya domin gano idan akwai ƙwayar cutar kwalara.
Hukumar daƙile cutaka masu yaɗuwa CDC ta ce yawanci ana maganin cutar ne cikin sauƙi ta hanyar bayar da ruwan gishiri a madadin ruwan jiki da mutum ya rasa sakamakon amai da gudawa.
Likitoci suna ba da maganin ORS mai ƙunshe da gishiri da suga da ake zubawa cikin gorar ruwa mai tsabta lita ɗaya a ba wanda ya harbu da cutar kwalara ya sha. Ana amfani da wannan maganin a faɗin duniya.
Idan kuma cutar ta yi ƙamari, za a buƙaci a yi wa mutum ƙarin ruwa.
Idan kuma jariri ne ya harbu da kwalara, za a ba mahaifiyar shawara ta ci gaba da shayarwa.
Mutane sai sun yi taka-tsantsan da wuraren da aka samu ɓarkewar kwalara. Amma mutum na iya kaucewa kamuwa da cutar a wuraren da ta ɓarke idan ya kiyaye.
Ga mazauna yankin da ke fama da annobar kwalara ko kuma baƙi, za su iya kiyaye shan ruwan roba ko ruwan da aka tafasa.
Mutum kuma sai ya tabbata ruwan da zai sha ba a buɗe marfin ruwan ba. Sai an ƙauracewa shan ruwan fanfo da kuma kayan zaƙi da aka sauya wa launi.
Sannan duk lokacin da mutum ya yi bayan gida ana so ya wanke hannunsa da sabulu haka ma idan zai ci abinci ya wanke hannunsa da sabulu.
Haka kuma a ƙauracewa cin abinci a kan hanya da kuma kayan marmari da aka fere. an fi son mutum yafere da kansa.
Wani shirin hukumar lafiya ta duniya WHO ya tsara yadda za a kawo ƙarshen kwalara da kusan kashi 90 zuwa 2030 a ƙasashe 20.
Kuma masu mutuwa a cutar a cewar WHO sun fi yawa a nahiyar Afirka fiye da sauran sassan duniya. Wannan kuma saboda rashin ingantaccen kiwon lafiya saboda ana iya magance kwalara cikin sauƙi ta hanyar ƙarin ruwa.
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)