play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right A shirye nake da na mutu domin Najeriya: muhimman batutuwa 9 da Buhari ya gabatar a jawabin ranar Demokradiyya

Siyasa

A shirye nake da na mutu domin Najeriya: muhimman batutuwa 9 da Buhari ya gabatar a jawabin ranar Demokradiyya

Bello Sani June 12, 2021 17


Background
share close

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a safiyar ranar Asabar, 12 ga watan Yuni, ya yi jawabi ga ‘yan Najeriya a ranar bikin dimokiradiyya ta bana, inda ya yi karin haske kan wasu muhimman ayyukan gwamnatoci da kalubalen tsaro da sauransu.

1. A shirye na ke in sadaukar da raina domin Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Asabar ya sha alwashin kare wanzuwar Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasa sannan kuma ya yi wasici da zaben gaskiya da adalci a 2023.

Ya ce:

“Ranar da na shiga rundunaar Sojan Najeriya na shirya sadaukar da raina saboda Najeriya. A matsayina na shugabanku, na ci gaba da jajircewa wajan kare wanzuwar Najeriya.”

2. Nan ba da jimawa ba dimokuradiyyar Najeriya za ta yi karfi
Shugaba Buhari ya ce dimokuradiyyar Najeriya za ta kasance a hanyar ci gaba a koyaushe da nufin isa ga balagaggiyar dimokradiyya, mai karfi, ci gaba kuma hadaddiyar kasa da za a lissafa ta a duniya.
3. Mun shawo kan wasu kalubale a cikin shekaru 2

Ya bayyana cewa a cikin shekaru biyu da suka gabata, Najeriya ta shaida kuma ta shawo kan yawancin kalubale wanda ka iya rusa sauran kasashe musamman wanda suka shafi tsaronmu baki daya.

4. Nan ba da dadewa ba gwamnatina za ta kawo karshen matsalar rashin tsaro a Najeriya

Shugaban kasar ya lura cewa duk wani abin da ya faru, duk da kankantar lamarin yana sa shi damuwa matuka, ya kara da cewa nan take ya umarci hukumomin tsaro da su hanzarta amma su kubutar da wadanda lamarin ya cika da su sannan kuma a gurfanar da masu laifin a gaban kuliya.

5. Wasu masu laifi na amfani da mawuyacin halin da ake ciki a Najeriya

Buhari ya bayyana cewa abin takaici ne, kamar yadda a yawancin lokutan da ake rikici wasu miyagun yan Najeriya kan yi amfani da mawuyacin halin sannan suna samun riba daga hakan tare da kuskuren cewa bin ka’idojin dimokiradiyya ya kawo cikas ga gwamnatinsa ta hanyar magance su gaba daya.

6. Ba da daɗewa ba za mu kamo masu laifi da ke aikata munanan abubuwa a Najeriya

Ya ce tuni gwamnatinsa take magance matsalolin kuma nan ba da jimawa ba za ta gurfanar da wasu daga cikin wadannan masu laifin a gaban kuliya.

7. Zan kara sa hannun jari a harkar Noma

Shugaban kasar ya kuma ce ayyukan da gwamnati da Babban Bankin Najeriya (CBN) ke jagoranta na haifar da bunkasar tattalin arziki a cikin shekaru 6 da suka gabata an fi mayar da hankali ne ga bangaren noma, aiyuka, kayayyakin more rayuwa, wutar lantarki da kuma bangaren kiwon lafiya na tattalin arzikin kasar.

8. Zan fitar da talakawan Najeriya miliyan 100 daga talauci

Buhari ya kuma lura cewa an aiwatar da hangen nesansa na fitar da talakawan Najeriya daga talauci cikin shekaru 10, ya kara da cewa ana iya ganin hakan a cikin shirin tallafi na kasa.

9. Mun cimma nasarori matuka kan bunkasa ababen more rayuwa

Shugaban kasar ya kuma bayyana cewa shirin gwamnatinsa na kawo sauyi a baben more rayuwa na ci gaba tare da muhimman ayyukan cimma nasarori masu mahimmanci a karkashin Asusun Bunkasa ababen more rayuwa na Shugaban kasa; Gadar Neja ta biyu, Babban titin Legas zuwa Ibadan da kuma babbar hanyar Abuja-Kaduna-Zariya-Kano.

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 10 ga watan Yuni, ya bayyana cewa makiyaya a Najeriya basa daukar komai sama da sanduna da adda don tara ciyawar shanun su.

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa shugaban a tattaunawarsa da ‘yan jaridu a yayin wata hira da gidan talabijin na Arise TV ya dage cewa makiyaya ‘yan asalin Najeriya basa amfani da manyan makamai kamar AK-47.

Da yake ci gaba da magana, shugaban na Najeriya ya bayyana makiyayan da ke dauke da muggan makamai cewa ba ‘yan Najeriya bane, tabbas daga wasu kasashen suke.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *