
Nnamdi Kanu: An ɗage shari’ar jagoran ‘yan a-waren Biafra saboda rashin bayyanarsa a kotu
Mai Shari’a ta Babbar Kotun Tarayyar Najeriya da ke Abuja, Binta Murtala Nyako, ta ɗage shari’ar jagoran masu rajin kafa ƙasar Biafra Nnamdi Kanu zuwa ranar 21 ga watan Oktoba mai zuwa. A ranar Litinin din nan ne aka so ci gaba da sauraron shari’ar Mr Kanu. Sai dai rashin […]