Hukumar Tace Fina-finai ta jihar Kano ta ce za ta fantsama cikin shafukan YouTube na yanar gizo domin yin farautar masu saka fina-finai da suka karya dokar hukumar.

Shugaban Hukumar, Isma’ila Na’abba Afakallah ya bayyana cewa hukumar ta gano cewa masu shirya finafinai suna fakewa da wannan dama domin kauce wa sharuddan hukumar.

” Mun gano wasu masu shirya finafinai na kauce wa bin dokokin hukumar suna saka fim batare da an duba shi a hukumar ba. Sannan hakan ya basu daman saka duk abinda suka ga dama, har da wadanda dokar hukumar bata amince da su ba.

Isma’ila Na’abba Afakallahu ya kara da cewa daga yanzu hukumar zata dira shafukan yanar gizo, wato shafin YouTube domin farautar ire-iren wadannan fina-finan.

Leave a Comment

%d bloggers like this: