Gwamnatin jihar Kaduna, a ranar Lahadi ta ce abinda ta mayar da hankali a kai shine tabbatar da ceto dalibai 39 da aka sace daga Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Afaka, ƙaramar hukumar Igabi, rahoton Daily Trust.

Tunda farko rahotanni sun bayyana cewa daliban da suka hada da mata 23 da maza 16 suna hannun masu garkuwar inda suke neman a biya su N500m kafin su sako su.

Gwamnatin jihar ta bakin kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, a ranar Lahadi ya ce sun jinjinawa ƙoƙarin jami’an tsaro wurin ceto daliban kwalejin 180.

Aruwan ya ce gwamnati jihar na tare da sojoji, DSS, yan sanda da sauran jami’an tsaro wadanda suka yi gaggawar kai ɗauki hakan yasa maharan ba su sace wasu daliban ba.

Leave a Comment

%d bloggers like this: