Gwamna Abdullahi Ganduje ya umarci dukkan wadanda suka fito takara a zabukan kananan hukumomi da ke tafe wanda aka shirya gudanarwa a ranar 16 ga watan Janairun sabuwar shekara, da su tabbata an yi musu gwajin shaye – shayen miyagun kwayoyi.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai bayani kan sakamakon taron majalisar zartarwa na jihar da aka gudanar a gidan gwamnatin Kano.

Malam Muhammad Garba, ya ce Gwamnatin jihar ta yanke shawarar yin hakan ne domin tsabtace jihar Kano daga shan miyagun kwayoyi.

Ya kuma sake jaddada aniyar gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na magance shan miyagun kwayoyi tsakanin shugabannin siyasa a fadin jihar Kano.

Leave a Comment

%d bloggers like this: