Singapore ta zama ƙasa ta farko da ta amince a riƙa sayar da naman da ake haɗa wa a daƙin gwaji.

Matakin ya buɗe kofa ga kamfanin Amurka na Eat Just ya riƙa sayar da naman ƙajin da yake haɗawa a cikin daƙin gwaji.

Ana samar da naman ne ta hanyar ƙwayoyin halittun dabobbi sannan a sarrafa su ta yadda za su sake girma a daƙin gwaji.

Mamallakin kamfanin mai suna Josh Tetrick ya ce naman da ɗaƙin gwajin ke samarwa ta wannan hanya ya fi lafiya da kuma dacewa da muhalli sama da wanda aka saba gani na kyankyasar ƙwai.

Wakiliyar BBC ta ce babu mamaki wannan ya ja hankalin sauran kamfanonin gogayya da ƙasashen duniya na aminta da wannan tsarin samar da naman.

BBC

Leave a Comment

%d bloggers like this: