FAAN tace ta samu labarin harin da ake shirin kaiwa tashoshin jiragen sama dake kasar nan daga ma’aikatar sufurin jiragen sama

Hukumar tashoshin jiragen saman Najeriya (FAAN) ta ce ta samu labari daga ma’aikatar sufurin jiragen sama akan yunkurin harin da ake shirin kaiwa filayen jiragen sama da suke fadin kasar nan.

FAAN ta gabatar wa da shugabannin tsaron tashoshin jiragen sama wannan sanarwar.

Kamar yadda takardar wacce TheCable ta gani ta ranar 9 ga watan Afirilun 2021, za a kai hari tashoshin jiragen sama da suke Kaduna, Maiduguri, Sokoto, Kano, Abuja da Legas.

An baiwa shugabannin tsaron tashoshin jiragen saman umarnin bayyana hanyoyi da dabarun kariya daga harin sannan an nemi su yi zaman gaggawa don samar da yadda za a bullo wa lamarin.

Karin bayani na nan tafe…kudai ko kasance da radio matasa.com domin kawo muku labarai da dumi diminsa.

Leave a Comment

%d bloggers like this: