Rundunar ‘yan sanda a jihar Edo ta cafke wani mai POS wanda ake zargi da taimakawa ‘yan fashi da makami da masu satar mutane wajen karbar kudi daga asusun bankunan wadanda lamarin ya cika da su.

An kama dan shekara 29 din mai suna Gadimoh Ofei Bright 29 a ranar Talata, 23 ga Maris, a Igarra da ke karamar hukumar Akoko-Edo bayan bincike na musamman ta hanyar bayanan sirri kan wani lamari na garkuwa da mutane, PM News ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa a kan lamarin da ake gudanar da bincike, an sace mutane da dama tare da yin fashi a yankin Ugbowo da ke cikin garin Benin.

An tura kudi daga asusun ajiyar wadanda abun ya cika da su a matsayin kudin fansa zuwa wani asusun banki kafin aka sake su.

Wata sanarwa daga mai magana da yawun rundunar yan sandan, SP Kontongs Bello, ya nuna cewa mai POS da aka kama ya furta cewa ya taimaka wa ’yan fashi wajen karbar kudi daga wadanda suka sace.

Ya ce ya karɓi kuɗin N1, 130,000 a cikin lamarin da ake bincike a kai daga dangin wanda abin ya shafa kafin aka sake shi.

Kayayyakin da aka kwato daga wurinsa sun hada da na’urorin POS guda biyu, katunan ATM guda 11 dauke da sunaye daban-daban, wayoyin hannu biyar da katinan SIM da kuma kudi N156,000.

Leave a Comment

%d bloggers like this: