Yan Najerya mazauna kasar Birtaniya sun gudanar da zanga-zanga a gidan gwamnatin Najeriya

A ranar Laraba, 31 ga watan Maris ne wasu ’yan asalin Najeriya mazauna kasar Birtaniya, suka gudanar da zanga-zanga a kan Shugaba Muhammadu Buhari, inda suka nemi ya koma gida.

Sashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa wasu ’yan Najeriya a Birtaniya sun taru a kofar gidan Gwamnati Najeriya da ke birnin Landan sannan kuma suka tare hanyar shiga ciki.

Masu zanga-zangar sun kasance dauke da kwalaye inda suka rika kira ga Shugaban kasar na Najeriya da ya koma kasarsa yayin da suka yi cincirindo a bakin Asibitin Wellington da ke birnin Landan.

Sun kirkiro maudu’i a shafin Tuwita mai taken #BuhariMustGo, wato dole Buhari ya sauka daga mulki, domin nuna bacin ransu kan abin da suka kira rashin iya gudanar da mulkinsa.

Da dama daga cikin al’ummar Najeriya sun bayyana bacin ransu kan tafiiyar Buhari kasar Birtaniya domin a duba lafiyarsa.

Wasu sun kira hakan a matsayin barnatar da kudin talakawan kasar masu biyan haraji yayin da wasu kuma ke sukar gazawar gwamnatin na inganta harkokin kiwon lafiyar da suka tabarbare, jaridar Aminiya ta ruwaito.

Leave a Comment

%d bloggers like this: