Yan Najeriya da dama na fargabar kasancewa cikin mawuyacin hali yayin da fashewar aman wuta daga wani dutse ya afkawa tsibirin Caribbean na St. Vincent da Grenadines wanda ke haifar da kaurar jama’a.

Akalla daliban Najeriya 230 ke karatun likitanci a tsibirin da kuma wasu masu yawon bude ido ke zaune a can.

Ya zuwa yanzu, Daily Trust ta tattara cewa an kwashe dubunnan mutane zuwa wurare masu aminci na tsibirin da kasashen makwabta ta hanyar amfani da bas da jiragen ruwa.

Karamin jakadan tsibirin a Najeriya, Dr Levi Odoe, ya nemi tallafi daga gwamnatin Najeriya da sauran masu fada a ji a duniya.

Akwai ‘yan Najeriya da yawa a tsibirin, kuma hakan na haifar da kalubale ga lafiya. Ana kwashe dangi zuwa wasu kasashe. Za mu yaba da taimako daga masu fatan alheri da abokan arziki,” in ji Dokta Odoe.

‘Yan kasar da ke cikin matsanancin hali sun watsa faifan bidiyo game da fashewar, wanda ya fara a ranar 9 ga Afrilu lokacin da bakin toka da hayaki ya turnuke sararin samaniya a kusan nisan kilomita 6.

Wani mai amfani da shafin Twitter, Rahym R. Augustin-Joseph ya wallafa a shafinsa na Twitter, @RahymRJoseph: “Mu tuna da sanya mutanen St. Vincent da Grenadines cikin addu’o’inmu a irin wannan lokacin da ake cikin na mawuyacin hali.”

St. Vincent da Grenadines suna da dutse mai aman wuta a tsaunin La Soufrière, wanda ya kai kololuwar mita 1,234.

Wannan shi ne karo na hudu da aman wutar dutsen ya afku a tsibirin bayan na farko da aka yi a shekarar 1718. Fashewa ta shekarar 1902 ta haifar da mutuwar mutane sama da 1000, yayin da fashewar 1979 ta lalata kadarorin da suka kai $ 100m.

Leave a Comment

%d bloggers like this: