An tabbatar da mutuwar mutane 10 sakamakon harin da Boko Haram ta kai Damasak

An tabbatar da rasuwar fararen hula 10 a harin da yan Boko Haram suka kai a daren ranar Talata a garin Damasak, hedkwatar karamar hukumar Mobbar na jihar Borno.

Shugaban karamar hukumar Mobbar, Mustapha Bako Kolo ne ya bayyana hakan kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Wasu da ke zaune a sansanin yan gudun hijira da ba a tabbatar da adadinsu ba suma sun jikkata sakamakon harin a cewar Kolo.

Duk da cewa dakarun sojojin saman Nigeria da sojojin sama sun dakile harin, wasu mutane fararen hula da dama sun jikkata.

cewar majiyoyi, yan ta’addan sun afka garin a motocci suka nufi inda sansanin sojoji ya ke a Damasak a yayin da mutane suka rika tserewa.

Harin na daren jiya a Damasak shine na biyu a cikin mako guda.

Yan ta’addan sun wallafa bidiyon harin da suka kai a karshen mako a Damasak inda suke kona gine-ginen Majalisar Dinkin Duniya da wuraren ajiye abinci.

Kawo yanzu da aka wallafa wannan rahoton, rundunar sojojin Nigeria bata yi tsokaci game da batun ba.

Leave a Comment

%d bloggers like this: