‘Diyar Ministar harkokin matan Najeriya ta fada hannun ‘Yan bindiga.

Wasu ‘yan bindiga sun sace wata Baiwar Allah wanda ‘diya ce a wurin Ministar harkokin mata na Najeriya, Madam Pauline Talen.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi garkuwa da Dapit Karen a unguwar Rantiya Lowcost da ke garin Jos, a karamar hukumar Jos ta Kudu, jihar Filato.

Wani daga cikin ‘yanuwan wannan Baiwar Allah ya tabbatar wa manema labarai aukuwar lamarin.

Majiyar ta bayyana cewa ‘yan bindigan sun shigo unguwar Rantiya Lowcost ne, su ka kutsa cikin gidan wannan mata a lokacin da mutane su ke sharan barci.

Kamar yadda ‘danuwan na ta ya bayyana, ‘yan bindigan sun zo ne da kimanin karfe 5:00 na safe.

Misis Dapit Karen wanda ta yi aure a Junairu ta na zaune ne tare da tsohuwarta a garin Jos, amma masu garkuwa da mutanen ba su dauki mahaifiyarta ba.

Kamar yadda ‘yanuwan na ta su ka bayyana, ‘yan bindigan sun kira su a wayar salula, sun bukaci a aika masu da Naira miliyan biyar a matsayin kudin fansar ta.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ba ta san wannan abu ya faru ba. Kakakin ‘yan sanda na jihar Filato, Ubah Gabriel, ya yi alkawarin za su binciki lamarin.

Mai girma Ministar harkokin mata ta kasa, Tallen ta na matsayin goggo ce a wurin Karen. Kafin yanzu Madam Tallen ta rike kujerar mataimakiyar gwamna a Filato.

Kun ji cewa masu garkuwa da mutane sun yi awon-gaba da fasinjojin mota a titin Takum-Wukari

A karo na biyu cikin watanni 3, an sake yin garkuwa da fasinjoji a wannan hanya a jihar Taraba. Wannan karo an dauke wani jariri da bai wuce shekara da haihuwa ba.

Akalla ‘yan bindiga 10 ne ake zargin sun tare wani titi a kusa da garin Chanchangi, a hanyar Takum zuwa garin Wukari, jihar Taraba, su ka sace matafiya kusan 10.

 

Leave a Comment

%d bloggers like this: