An sace wata budurwa ‘yar shekara 18 a gidan mahaifinta a wani yankin jihar Kebbi

A safiyar jiya ne wasu ‘yan bindiga suka sace wata yarinya‘ yar shekara 18 mai suna Naja’atu Faruk, a garin Birnin Kebbi da ke jihar Kebbi, Leadership ta ruwaito.

An sace Naja’atu daga gidan mahaifinta inda aka harbi wata mata Hajiya Nana Sanusi. Yanzu haka tana karbar kulawar likita a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Birnin Kebbi.

Mataimakin gwamnan jihar, Samaila Yombe Dabai wanda ya ziyarci gidan, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici kuma ya ba da tabbacin jajircewar gwamnati wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.
Ya kara da cewa babu wani abinda zai hana a gurfanar da masu aikata muggan laifuka a jihar.

 

Leave a Comment

%d bloggers like this: