Sarkin Anka ya ce an sace mutane fiye da 100 a jihar Zamfara a makon jiya. Sarkin Anka ya ce an sace mutane fiye da 100 a jihar Zamfara a makon jiya

‘Yan bindiga sun sace masu hake-haken ma’adanai a yankin Anka da Maru. Attahiru Ahmad ya ce hakan ya faru ne lokacin da aka sace yara a Jangebe

Mai martaba Sarkin Anka a jihar Zamfara, Attahiru Ahmad, ya ce masu hakar ma’adanai fiye da 100 aka sace tsakanin garin Anka da Maru kwanakin baya.

Alhaji Attahiru Ahmad ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun tsere da wadannan mutane ne a lokacin da su ka kawo masu hari a ranar 2 ga watan Maris, 2021.

Shugaban majalisar Sarakunan na Zamfara ya yi wannan bayani ne a garin Gusau, a lokacin da Janar Lucky Irabor ya jagoranci hafsoshin sojoji zuwa jihar.

NAN ta rahoto Sarkin ya na cewa wannan abu ya auku ne a lokacin da hankalin gwamnati ya karkata wajen ceto ‘daliban makarantar Jangebe da aka sace.

Mai martaba Attahiru Ahmad ya kara da cewa an kashe mutane 10 a lokacin da ‘yan bindigan su ka auka wa wani wuri da ake aikin hake-hake a jihar Zamfara.

Sarkin Anka, Ahmed ya ke cewa: “’Miyagun ‘yan bindigan su na ta kai wa wadannan masu aikin hako ma’adanai hari, su na tsere wa da kudinsu da dukiyoyinsu.”

Sarkin ya yi bayanin alakar masu aikin hako ma’adanai da ‘yan bindigan jihar, ya ce sun yi mamakin jin an hana jirgin sama tashi a Zamfara da ba ta filin jirgi.

A cewar Alhaji Attahiru Ahmad, idan gwamnati za ta sa wannan doka, ya kamata ta shafi sauran jihohin da ke fama da matsalar rashin tsaron da ta fi na Zamfara.

Leave a Comment

%d bloggers like this: