Miyagun ‘yan bindiga sun kaiwa fasinjojin dake kan hanyar zuwa Maulidin kasa a Sokoto hari

Fasinjoji dake kan hanyarsu ta zuwa Maulidin kasa dake jihar Sokoto sun shiga hannun masu garkuwa da mutane a kan hanyar Kankara zuwa Sheme dake jihar Katsina.

Majiyoyi da dama a yankin sun sanar da cewa basu san yawan wadanda aka sace ba yayin da jami’an ‘yan sanda suka ce babu wanda aka sace.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, wasu majiyoyin sun ce an sace mutum 70 inda wasu suka ce fasinjoji 50 ne aka yi awon gaba dasu.

Majiyoyin sun tabbatar da cewa lamarin ya auku ne wurin karfe 11 na daren Alhamis da jama’ar ke tafiya a manyan motoci kirar bas.

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya musanta aukuwar lamarin inda yace babu fasinjan da aka sace amma sun yi gaba da gaba da ‘yan bindiga sai suka tsere cikin dajika.

SP Isah yace an ga dukkan fasinjojin da suka tsere zuwa dajikan kuma sun kai 43 cif.

“Ba gaskiya bane. Abinda ya faru a daren Alhamis shine, an samu wasu fasinjoji daga jihar Gombe a kan hanyarsu ta zuwa Maulidi a Sokoto.

“A tsakanin Sheme da Kankara, ina tunanin ‘yan bindiga sun bullo musu amma sai suka bar ababen hawansu suka shiga daji domin tsira.

“Da safen nan jami’anmu tare da DPO suka shiga daji nemansu kuma duk an gansu a halin yanzu,” Isah yace.

Leave a Comment

%d bloggers like this: