Wasu bata gari da ake zargin ‘yan bindiga ne sun halaka mutane guda bakwai a wasu garuruwan jihar Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna a ranar Lahadi ta ce yan bindiga sun halaka mutane bakwai a sassa daban-daban a jihar, rahoton PM News.

Mr Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Lahadi a Kaduna.

– Wasu bata gari da ake zargin ‘yan bindiga ne sun halaka mutane guda bakwai a wasu garuruwan jihar Kaduna

– Mr Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, ya tabbatar da hakan a ranar Lahadi

– Gwamna Nasir El-Rufai ya yi bakin cikin samun rahoton ya kuma yi wa iyalan wadanda suka rasu ta’aziyya

Gwamnatin Jihar Kaduna a ranar Lahadi ta ce yan bindiga sun halaka mutane bakwai a sassa daban-daban a jihar, rahoton PM News.

Mr Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Lahadi a Kaduna.

Aruwan ya ce, “Cikin bakin ciki, jami’an tsaro sun bada rahoton cewa yan bindiga sun kai wa wasu mutane hari a kauyen Kajinjiri da ke karamar hukumar Igabi inda suka kashe mutane biyu.”

Ya ce wani mutum daya ya samu ranuka sakamakon harbinsa da bindiga da suka yi kuma ana jinyarsa a wani asibiti.

“Kazalika, a kauyen Rago da ke karamar hukumar Igabi, yan bindiga sun kashe mutanen garin biyu,” in ji shi.

Ya yi bayanin cewa a wani harin daban, yan bindiga sun kai hari Kutura Station, Karamar hukumar Kajuru, sun kashe mazauna garin uku.

Kwamishinan ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya yi bakin cikin samun rahoton ya kuma yi wa iyalan wadanda suka rasu ta’aziyya tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu.

Ya kuma yi wadanda suka jikkata sakamakon harin Kajinjiri fatan samun sauki cikin gaggawa.

Leave a Comment

%d bloggers like this: