Yan bindiga sun kashe wani masunci, Adamu Bala, a yayin da ya tafi rafi kama kifi a tsakanin Zango da Ungwan Ruhogo a karamar hukumar Zangon Kataf na jihar Kaduna, The Punch ta ruwaito.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Mista Samuel Aruwan, ya tabbatar da harin inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin amma bai bada karin bayani ba.

“A cewar rahoton, wasu mutanen da ba a sani ba sun kashe wani Adamu Bala bayan ya tafi rafi kama kifi a ranar Litinin 12 ga watan Afrilun 2021.

“An tsinci gawarsa a gabar rafi shekaran jiya Talata 13 ga watan Afrilun shekarar 2021.

“Gwamna Nasir El-Rufai ya yi bakin samun rahoton kuma ya yi wa iyalan wanda ya rasu ta’aziyya sannan ya yi addu’ar Allah ya jikan marigayin ya gafarta masa.

“A halin yanzu an fara bincike a kan lamarin.”

Leave a Comment

%d bloggers like this: