Yan bindiga sun afka Kwallejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara a jihar Niger

A kalla dalibi daya ne ya riga mu gidan gaskiya yayin da an kuma sace wasu da dama, Channels Television ta ruwaito.

An ruwaito cewa an sace wasu malaman kwallejin da iyalansu da ke zaune a rukunin gidajen ma’aikatan kwallejin.

Wani majiyar gwamnati da ya nemi a sakayya sunansa ne ya sanar wa Channels Television hakan ta wayar tarho a daren ranar Laraba.

A cewar majiyar, maharan sun afka Kwallejin KImiyya da Gwamnati da ke Kagaran ne misalin karfe 2 na daren ranar Laraba suka fara harbe-harbe.

A sakamakon harbin ne suka halaka dalibi daya sannan wasu da dama suka jikkata.

Sai dai majiyar bai iya tantance adadin mutanen da aka sace ba ko kuma wadanda suka samu rauni a lokacin hada wannan rahoton.
Majiyar ya kara da cewa wasu daga cikin yan bindigan sun saka kaya irin ta daliban makarantar domin kada a gane cewa su ba yan makarantar bane.

Wannan harin na zuwa ne kwanaki kadan bayan wasu yan bindigan sun kai wa wata motar fasinjoji hari a kan hanyar MInna zuwa Zungeru inda suka sace fasinjoji 21.

Amma daga bisani an ceto wasu daga cikin fasinjojin.

 

Leave a Comment

%d bloggers like this: