Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya ta ce ta kama wani boka da take zargi da kashe aƙalla ƙananan yara 9 ‘yan shekara 2 zuwa 4.

Ta ce an kama bokan ne da ke ƙauyen Rumbu a ƙaramar hukumar Ningi, bayan samun rahoton mutuwar wata yarinya mai suna Maimuna Isyaku wadda mahaifinta ya kai ta wajensa don ya duba rashin lafiyar da ke damunta.

Sai dai daga bisani ‘yan sanda sun gano gawarta a daji bayan mutumin ya shaida wa mahaifin Maimuna cewa ‘yarsa ta mutu lokacin da yake ƙoƙarin yi mata magani.

Mai magana yawun ‘yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Muhammed Wakil ya shaida wa BBC cewa mutumin boka ne da yake yi wa mutane magani.
A cewarsa, bayan ƙorafin da mahaifin yarinyar ya kai musu ne ya sa suka zurfafa bincike inda suka samu kama bokan wanda kuma ya kai su inda ya binne marigayiyar kuma bayan an kai sa ofishin ƴan sandan ne ya yi bayanin yadda lamarin ya faru.

“Mutane da yawa sukan kawo masa yaransu a kan cewa ba su da lafiya, an nemi magani ba a yi nasara ba shi yana amfani da wannan dama ce idan aka kawo sai ya kashe yaran, ya faɗawa iyayen yaran cewa a wajen yin magani yarinya ta rasa ranta”. in ji SP Wakil.

Ya bayyana cewa bokan ya tabbatar da cewa Maimuna ba ita kaɗai ya kashe ba, “akwai yaran da ya kashe kusan mutum guda huɗu”. A cewar SP Wakil, sun gano kayayyakin yara kusan 26 a wajen bokan.

Ya ƙara da cewa da zarar an kammala bincike, za su gurfanar da shi gaban kotu domin a yi masa hukunci daidai da abin da ya yi wa yaran.

Ku latsa alamar lasifikar da ke ƙasa don jin cikakkiyar tattaunawar da BBC ta yi da SP Ahmed Muhammed Wakil:

Leave a Comment

%d bloggers like this: