Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya buƙaci gawamnati ta sake nazari kan matakin Babban Bankin ƙasar (CBN) na rufe asusun ‘yan kasuwa da kamfanoni masu amfani da kuɗin intanet na cryptocurrency yana mai cewa yanzu lokaci ne da ya kamata a faɗaɗa tattalin arzikin Najeriya.

Ya kuma ce rashin ayyukan yi ga matasa ne babban ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta.

“A zahiri, ya ma wuce ƙalubale, buƙata ce ta gaggawa. Yana shafar tattalin arzikinmu da ƙara taɓarɓarewar matsalar tsaro a ƙasa,” in ji Atiku.

Leave a Comment

%d bloggers like this: