Rahoton kwararru a fannin lafiya da suka je binciken silar cutar corona a Wuhan, na cewa akwai yiwuwar Jemage ne ya fara yada cutar ga bil Adama ta hanyar wasu dabbobin cikin gida.
Wani babin binciken da kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP ya samo gabannin sake rahoton a hukumamnce, na kara nuna shakku kan camfin cewa cutar ta kubuce ne daga dakin gwaji .

Bincike da ya samu hadin gwiwar kwararru daga hukumar lafiya ta duniya da na kasar China, na shirin fita ne a lokacin da wani sabon nau’in cutar ke tilasta kasashen Turai tsaurara matakan yanki da annobar.

Leave a Comment

%d bloggers like this: