Salihu Tanko Yakasai, tsohon hadimin ganduje ya zargi Buhari da yin maganganu masu karo da juna.

Salihu Tanko Yakasai, tsohon mai bada shawara na musamman a fannin yada labarai ga gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari yana ruda ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a kasar nan da wa’adin da yake basu tare da jan kunne.

Yakasai, wanda Ganduje ya sallama a watan da ya gabata saboda kalubalantar mulkin Buhari da jam’iyyarsa ta APC, ya sanar da hakan ne a ranar Asabar.

A ranar Juma’a ne jaridar Legit.ng ta ruwaito yadda ‘yan bindiga suka kutsa kwalejin harkar noma da gandun dabbobi dake Kaduna suka kwashe dalibai.

An gano cewa jami’an tsaro sun ceto dalibai 180 amma 39 na hannun masu garkuwa da mutanen.

A ranar Asabar, mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya ce Buhari “ya bada jan kunne ga masu yunkurin zama ‘yan ta’adda da kuma ‘yan bindigan dake shiga makarantu. Ya ce kasar nan ba za ta bari a tabarbara mata harkar ilimi ba.”

A yayin yin martani ga kakakin shugaban kasan,Yakasai ya wallafa, “A gaskiyar magana, kana ruda ‘yan bindiga ko ‘yan ta’adda. A makon da ya gabata a Zamfara ka basu wa’adin watanni biyu, a yau kuma jan kunne ka bada, wanne za su dauka da gaske Mallam Garba?

Da a ce ni mahaifin daya daga cikin daliban makarantar kwana ne a cikin jihohin da lamarin ya shafa, zan cire da na ne kawai.”

Yakasai da ne ga dattaijon Kano, Tanko Yakasai, wanda a watan da ya gabata aka tsare shi a ofishin hukumar jami’an tsaron farin kaya a kan zarginsa da caccakar Buhari kan lamarin tsaron kasar nan.

 

Leave a Comment

%d bloggers like this: