Hedikwatar Rundunar Sojin Najeriya ta ce wani soja da yake cikin damuwa mai aiki a “202 Battalion of 21 Special Armoured Brigade Bama”, jihar Borno ya ruɗe ya kuma harbi wani jami’in soja ranar Laraba.

Muƙaddasshin Darkatan Sashin Huɗda da Jama’a na Rundunar Sojin Najeriya, Kanar Sagir Musa ya bayyana haka a cikin wata sanarwa ranar Alhamis a Abuja.

A cewar rahotonni, sojan ya kashe Laftanar Babakaka Ngorgi bayan da ya hana shi ya je ya ga iyalinsa.

Amma Mai Magana da Yawun Rundunar Sojin ya ce al’amarin ya afku ne lokacin da sojan ya je kusa da jami’in, wanda yake tsaye yana waya.

Ya ce a halin yanzu sojan yana tsare ana bincikar sa. Ya ce tuni an kai gawar jami’in da ya rasa ran nasa zuwa “7 Division Medical Services and Hospital”.

“Tuni an fara binciken al’amarin don gano dalilin da ya haifar da harbin. “Tuni an tuntuɓi iyalin marigayin.

“Rundunar Sojin Najeriya tana taya iyalin alhini a wannan lokaci na jarrabawa, kuma tana addu’a ga Ubangiji Maɗaukakin Sarki ya ji ƙan marigayin, ya ba iyalin haƙurin jure wannan rashi.

Leave a Comment

%d bloggers like this: