Wani magidanci da ake zargi da kashe matarsa saboda bakin kishi ya ce ya aikata hakan ne bayan ya sha tabar wiwi ta yi mishi karo.

Mutum wanda ya ce ya yi amfani shebur ne ya kashe matar tasa da dansa saboda sabanin da suka samu a lokacin da yake cikin maye, bai san abin da ya aikata ba sai da hankalinsa ya dawo mishi a ofishin ’yan sanda.
“ Wanda ake zargin yace na koma gida da rana ne domin in ba wa matata karin kudin cefane saboda ban bar mata isasshen kudi ba, amma sai na iske ta da wasu bakin mutane, wanda hakan ya kona min rai sosai saboda na yarda da ita.

Ta yi ta kokarin yi min bayani amma na ce atafau, na wuce na je na sha tabar wiwina ko zai kwantar min da hankali.

“Amma da na sha ta yi min karo sai na kasa danne zuciyata,” inji shi, a lokacin da ake gabatar da shi ga manema labarai kan lafin da ake zargi ya aikata a Hedikwatar ’Yan Sanda ta Jihar Anambra.

Ya yi zargin cewa shaidanin da ke tare da shi ne ya yi sanadin hallaka matar da dan nasa.

“Ban dawo cikin hayyacina ba sai da na bude ido na gan ni a ofishin ’yan sanda.

Leave a Comment

%d bloggers like this: