Wani kamfanin Amurka ya nemi afuwa kan sanya hoton masallaci mai dimbin tarihi a yankin Lamu na Kenya, a rigar mawakin Amurka Jay-Z, BBC Hausa ta rahoto.

Shugaban masallacin ya nuna adawarsa da rigar wanda ya ke cewa ana iya sanyata a wuraren da ake munanan ayyuka kamar mashaya.

– Biyo bayan sanya hoton masallaci a jikin rigir mawaki, shugaban masallacin ya nuna rashin jin dadinsa

– Kamfanin da ke da alhakin sanya hoton ya ba da hakuri tare da neman afuwan malaman masallacin

– Hakazalika kamfanin ya bayyana dalilin da ya sa ya sanya hoton masallacin mai duimbin tarihi

Wani kamfanin Amurka ya nemi afuwa kan sanya hoton masallaci mai dimbin tarihi a yankin Lamu na Kenya, a rigar mawakin Amurka Jay-Z, BBC Hausa ta rahoto.

Shugaban masallacin ya nuna adawarsa da rigar wanda ya ke cewa ana iya sanyata a wuraren da ake munanan ayyuka kamar mashaya.

“Mun karbi wasikar afuwan saboda anyi shi ne da zuciya guda,” a cewar malaman masallacin.

Mai kamfanin Zeddie Loky ya ce sun sanya tambarin masallacin ne a jikin rigar domin tallata yankin Lamu.

Lamu yankin ne mai dimbin tarihi kuma masallacin da aka gina tun a karni na 19 na jan hankalin masu zuwa yawon bude ido.

An ga Jay-Z sanye da rigar da ke nuna Masallacin Riyadha na Lamu a ranar 30 ga Maris, yayin da ya fito daga wani gidan abinci a Santa Monica, California.

CNN ta ruwaito cewa, Zeddie Loky da ya zana riga T-shirt din, wanda dan kasar Kenya ne, ya sanya hotunan a shafin Instagram, lamarin da ya jawo cece-kuce.

A ranar 3 ga Afrilu, Masallacin Riyadha ya sanya rubuta zuwa Loky a shafinsa na Facebook, yana cewa kwamitin gudanarwa da masu bauta a masallacin cewa:

“sun nuna damuwa kuma a zahiri sun ji an wulakantasu” da hotunan Jay-Z sanye da T-shirt, wanda ke dauke da hoton koren hoto na masallacin, tare da kalmar “Lamu” a samansa.

Leave a Comment

%d bloggers like this: