UNN ta dakatar da wani malaminta sakamakon zarginsa da dirkawa daliba ciki

Wani malami a jami’ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) da ke jihar Enugu, Dr Chigozie Jude Odum an dakatar da shi kuma an damke shi sakamakon cikin da ya dirkawa dalibar jami’ar.

An mayar da cewa za a dinga biyan malamin rabin albashi har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

An bayyana wannan hukuncin ne a wata wasika mai kwanan wata 15 ga Fabrairun 2021 wacce mataimakiyar rijistra ta makarantar, Mrs F. C Achiuwa tasa hannu.

Wasikar, wacce bata sanar da cewa dirkawa daliba ciki malamin yayi ba, ta ce an dakatar da malamin ne sakamakon zarginsa da ake yi da hantarar daliba tare da cin zarafinta.

Amma kuma, majiya makusanciya da jami’ar ta bayyana cewa malamin ya shiga wannan matsalar ne bayan ya dirkawa dalibarsa ciki.

Majiyar bata bada karin bayani ba a kan yadda lamarin ya auku, Daily Trust ta wallafa.

Leave a Comment

%d bloggers like this: