Wata kotun majistare dake zama a Ibadan, jihar Oyo, ta bukaci a adana mata gagararren shugaban masu garkuwa da mutane, Iskilu Wakili, a gidan gyaran hali a kan zarginsa da ake yi na kashe mutane, hada kai wurin cuta, garkuwa da mutane da fashi da makami.

An gurfanar da wanda ake zargin tare da wasu a gaban kotu sakamakon laifuka shida da ake zarginsu dasu.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an gurfanar da Wakili ne tare da Samaila, Aliyu Many da wani Abu mai shekaru 45 a duniya.

Legit.ng ta ruwaito cewa wasu jami’an OPC ne suka kwamushe Iskilu Wakili wanda ake zargi da zama gagarumin mai garkuwa da mutane.

Sai dai tun bayan da aka kama Wakili, ya musanta dukkan zargin da ake masa a gaban ‘yan sanda inda yace bai taba kisan kai ko garkuwa da mutane ba.

Leave a Comment

%d bloggers like this: