Fitaccen dan gwagwarmayar nan na Yarbawa, Sunday Adeyemo, ya fara tsokano kafa Jamhuriyar Oduduwa, yana barazanar kawar da ‘yan siyasar Yarbawa da zasu ki mara wa shirin nasa baya kafin 2023.

A wani faifan bidiyo da PRNigeria ta samu kuma aka fassara, Mista Igboho yayin da yake zantawa da shugabannin Yarbawa da matasa, ya ja kunnen ‘yan siyasan kan rashin nuna damuwar su ga Jamhuriyar Oduduwa.

A cewarsa, bai kamata ‘yan siyasar Yarbawa su yi ihun neman shugabanci na 2023 a wannan lokacin ba, sai dai su kasance a sahun gaba na shirin ballewar da shi da sauran ‘yan Kudu Maso Yamma ke goyon baya.

Lokacin da aka tuntube shi kan barazanar bidiyon Sunday Igboho, kakakin Hukumar tsaro ta farin kaya (SSS), Dokta Peter Afunanya ya shaida wa PRNigeria cewa hukumar leken asirin za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta a cikin ka’idojin da doka ta ba ta.

Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya ce:

“Idan da ku (masu rike da mukaman siyasa a Yarbawa) duk ba wakilai ne marasa amfani ba, ya kamata ku shugabance mu a gwagwarmayar ballewar. Amma kun shagaltar da yakin neman zaben Shugaban kasa mai zuwa. Lallai kun cika mahaukata.

“Ya kamata ku sani cewa bai kamata ku nemi zabe zuwa ofishin Shugaban kasa ba, ya kamata ku yi la’akari da hayaniyar mu (Yarbawa) kuma ku jagorance mu a fafutukar ballewar.

Leave a Comment

%d bloggers like this: