Daya daga cikin dalibai kashi na biyu da yan bindiga suka saki bayan sacesu da aka a makarantar ta FCFM dake Afaka, Kaduna, AbdulGaniyu Aminu, ya ce yan bindigan na hanasu Sallah kuma kullum suna bugunsu.

Bayani kan abubuwan da suka fuskanta cikin makonni uku da sukayi a daji, AbdulGaniyu ya ce bai taba shan wuya irin wannan a rayuwarsa ba.

Yayi wannan bayani ne jim kadan bayan gwamnatin jihar ta mikasu ga shugabannin makarantar.

“Cikin makonni uku da na yi a daji ban yi wani baccin kwarai ba. Ta yaya ma zakayi bacci saboda suna hanamu Sallah kuma suna zanemu tare da buga mana gindin bindiga,” yace.

A cewar Daily Trust, sunayen dalibai biyar kashi na biyu da aka sako sune Suzan Jatau, Ishaya Jafaru, Abdulganiyu Aminu, Haruna Aminu da Adamu Amin.

A jawabin kwamishana tsaro da harkokin cikin gidan jihar, Samuel Aruwan, ya yi kira ga daliban kada su yadda wannan ya karya musu gwiwa su ce zasu daina karatu.

Jiya kun ji cewa an sake sakin wasu dalibai biyar cikin 39 da aka sace a makarantar FCFM Afaka, jihar Kaduna.

Wannan ya biyo bayan mutum biyar da aka saki ranar Litinin.

Adadin daliban Afaka da aka saki yanzu ya zama 10, har yanzu akwai sauran 29 hannun yan bindiga.

Leave a Comment

%d bloggers like this: