Hedikwatar Tsaro ta Sojojin Najeriya ta ce ta yi nasarar kashe ‘yan fashi 50 a ƙauyen Kuriya da ke Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda ta Jihar Zamfara.

Sanarwar da Shugaban Sashen Yaɗa Labarai, Manjo Janar John Enenche, ya fitar a yau Lahadi ta ce dakarunsu sun gwabza da miyagun ne tare da taimakon jiragen sama.

Ya ƙara da cewa soja huɗu sun ji raunuka yayin fafatawar, inda suka ƙwato dabbobi guda 334 da ‘yan fashin suka sata.

A gefe guda kuma, wasu dakarun da aka tura garin Duniya da ke Ƙaramar hukumar Danmusa ta Jihar Katsina sun ƙwato dabbobi 62 daga ‘yan fashi, waɗanda suka tsere bayan sun hangi dakaru.

Leave a Comment

%d bloggers like this: