Wasu da ake zargin ‘yan fashi ne sun kai hari garin Anune a karamar hukumar Makurdi ta jihar Benuwe

Sojojin Operation Whirl Stroke (OPWS) sun kashe wasu yan fashi da makami su biyar da suka kai hari kan wani gari a ƙaramar hukumar Makurdi ta jihar Benuwe, Daily Trust ta ruwaito.

Jaridar ta ce sojojin sun kai farmaki maboyar ‘yan fashin a kan iyakokin jihohin Benuwe da Nasarawa a ranar Asabar, 17 ga Afrilu.

Legit.ng ta tattaro cewa yan fashin sun far ma mazauna kauyen Anune, wani garin karkara a wajen karamar hukumar Makurdi, kuma sun kashe wasu mutane da ba a bayyana adadin su ba.

Wani ganau ya ce an ga wani jirgin sojin sama mai saukar ungulu yana shawagi a kusa da kauyen da abin ya shafa tsakanin karfe 9 na safe zuwa 10 na safiyar Asabar, a daidai lokacin da sojoji da ‘yan sanda ke ta yawo a cikin manyan motoci.

Shaidar ya kara da cewa jami’an tsaro sun shiga cikin dajin da ‘yan ta’addan suka tsere sannan kuma ba da dadewa ba, sai aka ga sojoji ’sun dawo tare da akalla gawarwakin mutane biyar da ake zargin na yan fashin ne.

A halin da ake ciki, kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Benuwe, DSP Catherine Anene, ta tabbatar da harin kan kauyen Anune amma ba ta bayyana ko akwai wadanda suka rasa rayukansu ba.

Anene ta ce an tura tawagar jami’an ‘yan sanda yankin don dakile ci gaba da karya doka da oda.

Leave a Comment

%d bloggers like this: