Sojojin kasa tare da taimakon jiragen sama na rundunar sojin sama sun yi bata kashi da ‘yan ta’addan Boko Haram a Damasak, hedkwatar karamar hukumar Mobbar na jihar Borno.

Kafar watsa labarai ta PRNigeria ta tattaro cewa ana zargin wasu daga cikin yan ta’addan suna kan kwasar ganima yayin da suka afka wa rumbunan ajiyar kungiyoyin agaji na kasa da kasa a cikin motocinsu.

Wani jami’in leken asiri ya ce ‘yan ta’adda sun zo a cikin manyan motocinsu suna kai hari kan rumbunan ajiyar kafin isowar jirgin sojan.

“Labari mai dadi shine cewa jirgin rundunar sojin sama ya kai mu su hari ta sama yayin da aka jibge sojojin kasa a wasu wurare masu muhimmanci suna musayar wuta”, in ji majiya

Leave a Comment

%d bloggers like this: