Shugaban majalisar dattijai ya bayyana cewa, talakawa baburuwansu da batun raba kasa

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya ce fitattun mutane ne ke ingiza Najeriya zuwa ga wargajewa, The Cable ta ruwaito.

Da yake zantawa da manema labarai ranar Asabar, Lawan ya ce talakawa na ganin cewa ya kamata kasar ta ci gaba da kasancewa a matsayin dunkulalliya da ta fi karfin ballewa.

“Na yi imanin cewa yawancin ‘yan Najeriya sun yi imanin ya kamata su kasance a inuwa daya – ina nufin talakawan Najeriya,” in ji Lawan a garinsu, jihar Yobe.

“Wadannan mutane ne da suka yi imani da hadin kan kasar nan. Amma fitattu nan ne inda matsalar take.

Fitattun mutane za su gaya muku cewa, a’a, dole ne mu balle. Na yi imanin cewa ya kamata mu yi adalci ga dimbin ‘yan Najeriya – musamman talakawan Najeriya.”

Shugaban majalisar dattijan ya kara da cewa talakawa na son a jagorance su yadda ya kamata – kuma “dole ne mu ba su jagoranci na adalci.”

Ya ce ya kamata a ko yaushe a magance korafin wadanda ke kiran ballewa amma ya kara da cewa: “Wannan ba shi ne zai zama sanannen matsayin mutane daga kowane bangare na kasar ba.”

“Don haka, na yi imanin cewa hadin kan kasar nan ba abu ne da za a tattauna ba,” in ji shi.

Sanarwar ta Lawan ta sake bayyana ra’ayin Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya dage kan cewa Najeriya ta fi karfi a dunkule maimakon a wargaje.

Kamar dai yadda kiraye-kirayen ballewa suka ta’azzara a ‘yan makwannin nan, shugaban ya ci gaba da maimaita kudurinsa na ganin cewa Najeriya ba za ta rabu ba.

Leave a Comment

%d bloggers like this: