Gwamnatin tarayya zata tilasta dokar dakatar da albashi matsawar ma’aikaci bai yi aikinsa ba ga kungiyar likitoci masu neman kwarewa na Najeriya basu koma kan ayyukansu ba.

Ministan ayyuka da kwadago, Chris Ngige ne ya sanar da wannan jan kunnen a ranar Juma’a a wata tattaunawa da gidan talabijin din Channels.

“A ranar Talata, zan gayyacesu don su koma kan ayyukansu. Zan sanar dasu cewa matsawar ba su yi aiki ba gwamnati ba za ta biyasu ba,” cewar Ngige.

Wadanda aka dauka aiki ya kamata su dage wurin kulawa da lafiyar marasa lafiya. Za mu iya neman likitocin gargajiya, bana fatan mu kai nan wurin amma in dai aka kai toh za mu yi amfani da tsumagiyarmu.”

 

Leave a Comment

%d bloggers like this: