Shugaban kasa Muhammadu ya amince da sabunta nadin Alex Okoh, shugaban BPE

Sanarwar sabunta nadin ta fito ne daga bakin babban hadimin shugaban kasa a fanin kafafen watsa labarai, Laolu Akande

Sabunta nadin da aka yi wa Mr Alex Okoh za ta fara aiki ne daga ranar 10 ga watan Afrilun shekarar 2021

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da sabunta nadin Mr Alexander Ayoola Okoh a matsayin shugaban hukumar sayar da hannun jari, BPE, karo na biyu na tsawon wa’addin shekaru hudu, Vanguard ta ruwaito.

Sanarwar sabunta nadin ta fito ne daga bakin babban mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan kafafen watsa labarai, ofishin mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande.

Akande ya yi bayanin cewa nadin ya yi dai-dai ta sashi na 17 (1) (a) da (2)(a) na Public Enterprise (Privatization & Commercialization) Act, 1999.

Sabunta nadin zai fara aiki daga ranar 10 ga watan Afrilun shekarar 2021 a cewar sanarwar.

Hukumar BPE ma’aikata ce ta gwamnatin tarayya da ke kula da sauya-sauye na tattalin arziki musamman sayar da kadarori/kamfanonin gwamnati ga yan kasuwa da za su inganta su.

BPE kuma ita ce sakatariyar Cibiyar Sayar da Kadarori/Kamfanonin gwamnati na kasa.

Leave a Comment

%d bloggers like this: